Labarai

Wike yace Masu tallace-tallace ne ke haddasa rashin tsaro a Abuja

Wike yace Masu tallace-tallace ne ke haddasa rashin tsaro a Abuja.

Sabon minista

Acikin shirin namu nayau zakuji cewa, Sabon Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja a Najeriya, Nyesom Wike ya haramta tallace-tallace a titunan birnin.

yana mai cewa, masu tallar da suka hada da masu sayar da masara na taka rawa wajen tabarbarewar tsaro da kuma aikata miyagun laifuka a birnin.

Wike

Wike ya bayyana haka ne kai-tsaye a yayin da yake jawabi ga tawagar shugabannin jami’an da ke kula da al’amurran babban birnin da kuma bunkasarsa.

Wike wanda tsohon gwamnan jihar Rivers ne ya bukaci jagororin da su rika aiwatar da abin da ya dace.

Abu mafi muhimmanci shi ne, dole ne mu aikata wannan domin tabbatar da cewa, Abuja ta maido da martabarta.

Na kewaya sassan Abuja, kuma na gano cewa, akwai duhun rashin wutar lantarki a wurare masu yawa.

Abin da za mu yi

Wike yace Masu tallace-tallace ne ke haddasa rashin tsaro a Abuja
Wike yace Masu tallace-tallace ne ke haddasa rashin tsaro a Abuja

Abin da za mu yi shi ne, tabbatar da samuwar wutar lantarki nan ba da jimawa ba.

Ministan ya bukaci kawo karshen ajiye motoci barkatai a birnin, yana mai cewa, dole ne a dauki mataki nan kusa.

Ministan ya kara da cewa, masu sayar da masara na zubar da totuwarsa a ko ina, kuma hakan ne ke haddasa matsalar tsaro.

Miyagu na zuwa sayen masara kuma suna amfani da damar wajen leken asiri tare da bayar da bayanai ga wasu miyagun. Dole ne mu share masu talla daga tituna a cewarsa.

Muna rokon Allah subhanahu wata’ala da yayimuma sauƙi wannan matsala da tsadar rayuwa da take addabar mutane Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

Danna Nan: Matsaloli tsaro 3 da suka addabi Nijar bayan juyin mulki

Mungode da bibiyar wannan shafin namu mai albarka.

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook Page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button