Labarai

Shuwagabannin 8 da suka halarci taron tattaunawa akan dawo da mulkin Nijar a hannun Bazoum

Shuwagabannin 8 da suka halarci taron tattaunawa akan dawo da mulkin Nijar a hannun Bazoum

An buɗe taron tattauna amfani da ƙarfin soja ko diflomasiyya a kan Nijar

Shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma sun buɗe taron ƙoli a Abuja a ƙoƙarin da suke yi na yanke shawarar ko su yi amfani da ƙarfin soja ko diflomasiyya da nufin mayar da Nijar kan tsarin dimokraɗiyya, bayan juyin mulkin watan Yuli.

Juyin Mulkin Nijar

Mako biyu kenan da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suka hamɓarar da Bazoum Mohamed daga kan mulki tare da tsare shi – a wani al’amarin juyin mulkin soji na baya-bayan nan da ke naso a faɗin nahiyar Afirka.

Shugabannin da suka isa Abuja don wannan taro sun haɗar da:

Shugaban Saliyo, Julius Maada Bio

Shugaban Guinea Bissau, Umaro Mokhtar Sissoco

Shugaban Burundi Everiste Ndayishimiye

Shugaban Kwatdebuwa Alassane Ouattara

Shugaban Mauritania Mohamed Ould Ghazouani

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo

Shugaban Senegal Macky Sall

Shugaban Benin Patrice Talon

Shugaban Najeriya kuma shugaban Ecowas Bola Tinubu.

Babu dai wani zaɓi mai sauƙi ga shugabannin na Ecowas, da Tinubu ke jagoranta.

Akwai matsin lamba a kansu na ganin sun mayar da tsarin dimokraɗiyya a Nijar – wata makekiyar ƙasa da ke fama da ɗumbin matsaloli kamar rikicin ‘yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi da kuma talauci.

Sojojin da suka ƙwace mulki a Nijar ya zuwa yanzu sun yi ƙesasa ƙasa kan duk wani matsin lambar tattalin arziƙi da na diflomasiyya.

Ƙungiyar ta kuma yi barazanar amfani da ƙarfin soja. A ‘yan shekarun baya, wannan na iya zama wani zaɓi da babu wata taƙaddama kansa.

Amma yanzu sauran ƙasashe masu maƙwabtaka da Nijar musamman Mali waɗanda a baya-bayan nan suka faɗa ƙarƙashin mulkin sojoji kuma suke samun tallafi daga sojojin hayar Rasha, suna goyon bayan janar-janar ɗin da suka yi juyin mulki a Nijar.

A jawabin buɗe taro da ya gabatar, shugaban ƙungiyar Ecowas, ya faɗa wa shugabannin da ke halarta cewa wa’adin kwana bakwai da suka bai wa shugabannin juyin mulkin Nijar, kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba.

Ya kuma shaida musu cewa ƙungiyar Ecowas ta yi amfani da hanyoyin diflomasiyya don cimma masalaha.

Ya ce ya yi farin cikin cewa ƙwararren jami’in diflomasiyya, Babagana Kingibe da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III da Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) sun halarci taron don bai wa shugabannin ƙasashen ƙungiyar ƙarin haske a kan ƙoƙarin shiga tsakani.

A cewarsa, jami’an sun halarci Libya da Aljeriya, inda suka samu tarba daga shugabannin ƙasashen masu maƙwabtaka da Nijar

Shuwagabannin 8 da suka halarci taron tattaunawa akan dawo da mulkin Nijar a hannun Bazoum
Shuwagabannin 8 da suka halarci taron tattaunawa akan dawo da mulkin Nijar a hannun Bazoum

Tinubu ya kuma bayyana cewa bisa matsayar da suka cimma a taronsu na farko, manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas sun yi taro daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Agusta, kuma za a gabatar musu da shawarwarin da suka bayar da ma wata muƙala da shugaban Hukumar Ecowas ya gabatar kan halin da ake ciki a Nijar.

Amma mizakace dangane da wannan lamarin.

Danna Nan:Ahmad Musa Ya taimake ɗan Film baba karkuzu da maƙuddan Kuɗaɗe

Domin Karin Bayani Kuyi Following ɗin :HausaOne Facebook page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button